9 Faburairu 2019 - 19:44
An Bude Taron Kasashen AU A Karo Na 32 A Kasar Habasha

Yau Asabar, shuwagabannin kasashen Afrika, sun bude taronsu na shekara-shekara, a birnin Adis Ababa, na kasar Habasha

Taron wanda shi ne karo na 32, zai maida hankali kan batutuwa da suka hada tsaro, rikicin Libiya, tattalin arziki da kuma halin da dubban ‘yan gudun hijira ke ciki a kasashen da suka koma, da kuma wadanda rikici ya raba da muhallansu a cikin kasashensu.

Daga cikin shuwagabannin da zasu halarci taron harda shugaba sabon shugaban Jamhuriya Demukuradiyyar Congo, Félix Tshisekedi, da kuma Abdel Fatah Al-Sisi, na Masar, wanda shi ne zai karbo shugabancin karba karba na kungiyar daga hannun takwaransa na Ruwanda, Paul Kagame.

Bayanai sun ce daya daga cikin batutuwan da sabon shugaban kungiyar Abdel Fatah Al-Sisi, zai sa a gaba sun hada da matsalar tsaro da yaki da ta'addanci da kuma halin da kasar Libiya ke ciki.

Hakazalika kuma masana na ganin Masar, zata taimaka wajen cimma nasara kan yarjejeniyar cinikaya marar shinge a tsakanin kasashen na AFrika da har yanzu take tangal-tangal.

kafin hakan dama shugaban hukumar Tarayyar ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, su matsa kaimi wajen tabbatar cimma yarjejeniyar.

Har ila yau, ya ce yana fatan kasashe 6 da suka rage ba su amince da yarjejeniyar ba, za su sanya hannu nan ba da jimawa ba, kana wadandan suka riga suka sanya hannu kuma, za su gaggauta aiwatar da ita.